Hajjin 2022: Masari ya tura tawaga Saudiya domin kama masaukin alhazan Katsina

0
430

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya tura tawaga zuwa Saudi Arebiya domin kama wa alhazan jihar masauki da tanadar musu da sauran Ababen more rayuwa ingantattu.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar Jin daɗi da Walwalar Alhazai ta jihar, Badaru Bello Karofi ya fitar a yau Alhamis.

Ya ce Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Muntari Lawal, da Babban Daraktan Hukumar Jin dadin Alhazai ta jihar, Alhaji Suleiman Nuhu kuki ne su ka jagoranci tawagar

Da ga cikin tawagar kuma akwai Daraktocin Hukumar wadanda suka hada da Daraktan kudi na Hukumar Alhaji Sagir Abdullahi inde Hakimin Musawa da Daraktan Operations Alhaji Auwal Masari da Kuma Darakta Monitoring na Hukumar Alhaji Yusuf Ahmed.

Sanarwar ta ce hakan wani kokari ne na gwamnatin na ganin cewa alhazan jihar sun samu hidima ingantacciya a ƙasa mai tsarki yayin aikin Hajjin na bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here