Ƙungiyar mai zaman kanta da ke kawo Rahotanni da sa ido kan Aikin Hajji da Ummara, IHR, ta buƙaci Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON, da ta bi ka’idojin da ta gindaya wajen zaɓar kamfanonin jiragen da ba za su yi watsi da maniyyata ba kafin da kuma bayan gudanar da aikin Hajjin 2022.
Kungiyar ta kuma yi kira ga kwamitin tantancewar da hukumar ta kafa da ya yi la’akari da ma’auni, tarihin ƙwazo da kuma gazawa, halin da irin wadannan kamfanonin jiragen sama su ke a yanzu, da kuma karfinsu da kyawun sh na iya yin jigila daidai da jadawalin jigilar jirage.
Shugaban IHR na ƙasa, Malam Ibrahim Mohammed ne ya yi wannan kira a wata sanarwar da ya fitar a yau Litinin.
Ƙungiyar ta tuno cewa hukumar ta kafa wani kwamiti domin tantance kamfanonin jiragen da suka nemi jigilar maniyyata aikin hajjin 2022 daga Nijeriya.
“Kada kwamitin ya sarayar da aminci da kwarewa don rage farashin jirgin domin irin wannan matakin ba zai haifar da ɗa mai ido ba ga ayyukan Hajji,” in ji IHR.
Sannan ta dorawa kwamitin tantancewar NAHCON alhakin yin biyayya ga sashe na 6 a karkashin AIYUKAN DA SU KA WAJJABA A KAN KAMFANIN JIRGI a cikin yarjejeniyar da ta kulla da masu jigilar Alhazai.
IHR ta kuma yi kira ga NAHCON da ta tabbatar da cewa ba a ba da kwangilar kamfanonin jiragen sama ga bara-gurbi ba.
Kwamitin ya kamata ya zaɓi daga cikin shahararrun kamfanonin jiragen sama waɗanda ke da jiragen sama da ma’aikata a shirye don turawa a kowane lokaci.