Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta kafa kwamitin tantance hakikanin kuɗin aikin Hajjin 2022.
Kwamitin da ya yi zama jiya a ofishin NAHCON da ke unguwar Ummuljud a garin Makkah, an ɗora masa alhakin Tantance da lissafa kuɗaɗen Hajji na 2022 da ya shafi hidimomin alhazai na cikin gida.
Kwamitin ya ƙunshi Daraktan gudanarwa na NAHCON, Dakta Sodandgi da Sani Titilayo mai wakiltar NAHCON.
Sauran sun haɗa da Sakataren zartarwa na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano Alh Abba Muhammad Dambatta, Tawagar sa ta Jihar Neja Alh Labaran Maku mai wakiltar Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jiha.