Hukumar Jin daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta gargaɗi maniyyatan jihar da su yi hankali da ƴan damfara idan su ka je Saudiya.
Daraktan wayar da kai da ilamantarwa na hukumar, Alhaji Nuhu Salihu Dambatta, shi ne ya yi jan hankalin yayin da ya jagoranci jami’an hukumar zuwa cibiyoyin bita na Ƙananan Hukumomin Rogo, Karaye da kuma Gwarzo.
Dambatta, yace faɗin hakan ya zama wajibi, duba da cewa mafiya yawan maniyyatan na bana sababbin alhazai ne wadanda basu da gogewa kan harkokin aikin Hajji.
Ya ce hukumar na yin iya bakin kokarinta wajen daukar matakan da su ka wajaba don kare alhazan daga fadawa hannun muyagun mutane, don haka ya jaddada bukatar da ake yi musu na tuntubar jami’an alhazai na kananan hukumominsu.
Ya kuma yi kira ga maniyyatan da su je gurin duk wani wanda suka tabbatar jami’in hukumar ne domin yi musu jan gora kan duk wani abu da ya shige musu duhu.
Malam Nuhu Garba Dambatta, yayi amfani da taron wajen yabawa maniyyatan kananan hukumomin na Rogo, Karaye da Kuma Gwarzo, bisa yadda suka kasance masu bin doka da kuma jajircewa wajen halartar bitar inda yay fatan zasu dore da yin hakan har a can kasa mai tsarki.