Kamfanin Sufurin Jiragen sama, EgyptAir ya sanar da fara shin tikitin jirgi na Hajjin bana, wanda ya fara da ga
LE16,990 da ga Cairo zuwa Jeddah, zuwa da dawo wa a ɓangaren gama-gari.
Ɓangaren masu kuɗi kuma ya fara da ga LE18,990.
Kamfanin, a wata sanarwa a yau Alhamis, ya sanar da cewa farashin tikitin da ga Cairo zuwa Madina a jiragen Cairo zuwa Jeddah, zuwa da dawo wa, farashinsa LE17,990 na matakin gama-gari, sai kuma LE19,990 na ɓangaren masu kuɗi.
Kamfanin ya baiyana cewa zai ci gaba da karɓar ajiye guraben tikitin Hajji daga kamfanonin jigilar jirgin sama masu zaman kan su har zuwa Alhamis, 26 ga watan Mayu ta sashin Hajji da Ummara na kamfanin.