Shugaban Kwamitin Daraktoci da ke kula da Hukumar da ke Kula da Alhazzai na Cikin gida, Saed Al-Juhani ya bayyana ranar da ake sa ran cewa maniyyata za su fara neman guraben aikin Hajjin shekarar 2022.
Al-Juhani ya bayyana haka ne a wata hira da tashar Al-Ekhbariya ‘, inda ya ce ana sa ran mahajjatan cikin gida za su sami damar yin ajiye guraben biyan kuɗaɗen aikin Hajji a farkon mako mai zuwa.
A kwai tsare-tsare guda uku na aikin Hajjin ns bana waɗanda kamfanonin aikin hajji na cikin gida suka gabatar.
1 – Hasumiyar Hajji a cikin yankin Mina.
2 – Kunshin Deyafah1, mai dauke da tanti na zamani masu kama da dakunan otal, wadanda ake ganin za su bayyana a karon farko a aikin Hajjin bana.
3 – Kunshin Deyafah2, wadanda su ne tantuna na yau da kullun waɗanda aka tanadar da dukkan kayan aiki.
Al-Juhani ya tabbatar da cewa, abincin da za a bai wa mahajjatan cikin gida, na ƴan ƙasa da mazauna, zai kasance sabbin abinci ne waɗanda suka dace da kunshin da ma’aikatar Hajji da Umrah ta amince da su.
Haka tsarin da aka bi wajen samar da abinci ga mahajjata a shekarun da suka gabata, musamman a shekara ta 1440 bayan hijira, za a yi amfani da shi a lokacin aikin Hajjin bana ta yadda za a samu damar mahajjaci ya zuba abinci da kan sa ga mahajjata.
Dangane da adadin da aka ware na bana ya zuwa yanzu, adadin da aka amince da shi ya kai 150,000 na mahajjata na gida, ƴan kasa da mazauna gida, in ji Al-Juhani, yana mai nuni da cewa idan aka samu kari za a sanar.