Hajjin 2022: Yau za a fara yi wa maniyyata 1,562 alluran rigakafi a Legas

0
252

Yayin da a ke tunkarar ranar fara jigilar alhazai zuwa Saudi Arebiya, a shirye-shirye da ta ke yi na Hajjin bana, gwamnatin Jihar Legas, za ta fara gangamin allurar rigakafi ga Maniyyata 1,562.

Hukumar Jin daɗin Alhazai Musulmai ta Jihar ce ta bayyana haka a wata sanarwa.

Gwamnatin jihar ta ce za a yi rigakafin ne domin kare alhazan jihar da ga kamuwa da cuttuka a yayin zuwa da dawo wa daga aikin Hajjin.

Kwamishinan Harkokin Cikin Gida, Anofiu Elegushi, ya bayyana cewa yin rigakafin wani mataki ne mai muhimmanci s dokokin da Saudiya ta shinfida kafin tafiya ƙasa mai tsarki.

A taron kwamitin amintattu, ya ce ko wanne maniyyaci zai karbi rigakafin shawara, ɗigon shan-inna da kuma na sanƙarau, inda ya ce hakan zai yi daidai ne da sharuɗɗan tafiya ƙasashen waje domin kariya daga ɗaukar cututtuka masu yaɗuwa.

Ya ce za a fara allurar rigakafin ne a yau Litinin, 30 ga watan Mayu, a kuma kammala a ranar 2 ga watan Yuni, inda ya ƙara da cewa aikin zai gudana ne a a a babban dakin taro na Masallacin Shamsi Adisa Thomas (SAT) da ke unguwar GRA, Ikeja, Legas.

Kwamishinan ya yi kira ga dukkan Maniyyata da su tabbata sun je an yi musu rigakafin domin gudun samun matsala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here