Hajjin 2022: Hukumar Alhazai ta Abuja ta samar da ganganriyar masauki ga maniyyatanta

0
375

Hukumar Alhazai ta Babban birnin Tarayya Abuja ta tanadi masaukin da ya dace da maniyyatan bana a birnin Makkah na kasar Saudiyya.

Daraktan Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Babban Birnin Tarayya, Malam Muhammad Nasiru Danmallam ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke karɓar rahoton tantance maniyyatan da za su yi aikin Hajjin bana daga babban birnin tarayya ,Abuja.

Mallam Danmallam ya ce masaukin na nan a unguwar Hafa’ir da ke da tazarar mitoci 800 daga masallacin Harami na Makkah.

Daraktan ya bayyana cewa wurin zai baiwa tawagar Babban Birnin Tarayya damar gudanar da sallolinsu na farilla guda biyar a babban masallacin cikin sauki.

Ya bayyana cewa hukumar babban birnin tarayya Abuja ta hannun Ƙaramar Ministar, Dr Ramatu Tijjani Aliyu ta dukufa wajen ganin cewa maniyyatan da suka fito daga yankin sun samu ingantacciyar hidima idan aka kwatanta da sauran jihohin tarayya.

Ya bayyana cewa, saboda kishinta na kyautatawa maniyyatan babban birnin tarayya Abuja, mai girma ministar, Dr. Ramatu Tijjani A, ta yi alkawarin bayar da duk wani tallafin da ya dace domin gudanar da aikin hajjin bana cikin nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here