Gwamnatin Jihar Katsina ta ce ta tanadi masaukai masu kyau ga maniyyatanta a kusa da Masallacin Harami na Makka a Hajjin 2022.
Babban Daraktan Hukumar Jin Daɗi da Walwalar Alhazai ta Jihar Katsina, Alhaji Suleman Nuhu Kuki ne ya bayyana haka a wani taron ganawa da jami’an aikin Hajji na shiyyoyi, mataimakansu, masu gudanarwa da ma’aikatan hukumar domin duba a kan irin shirye-shirye na Hajjin bana.
Kuki, wanda dawowar sa kenan da ga ƙasa mai tsarki domin shirye-shiryen yi wa akhazan jihar hidima a yayin aikin Hajji, ya kuma yi jawabi a kan kudaden ajiya da maniyyata su ka biya, gwaje-gwaje na lafiya da kuma yin biyayya da sharuɗɗan da NAHCON da Saudi Arebiya su ka gindaya.
Ya kuma yaba wa ma’aikatan hukumar a bisa sadaukarwar su, inda ya ƙara musu ƙaimi da su ƙara dage wa domin samun nasarar aikin Hajjin bana.
Babban Daraktan ya kuma nuna gamsuwa bisa yadda Maniyyata su ka cika ƙa’idar ɗaukar allurar rigakafin korona ta ɗaya da ta biyu har da ma ta uku.
Ya kuma yaba wa gwamnatin Jihar Katsina, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari da kuma hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON domin jajircewar su wajen samun nasarar Hajjin bana.