Kwamishina a Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON, mai kula da Shiyyar Kudu-maso-Kudu, Alhaji Sadiq Musa, ya bayyana cewa Shiyyar na baiwa hukumar haɗin kai wajen shirye-shiryen Hajjin bana.
A wata ganawa da ya yi da Kanfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a yau Talata, Musa ya ce duk wasu shirye-shirye an kammala su domin inganta aikin Hajjin na bana ga alhazan shiyyar.
A cewar sa, irin gudunmawar da gwamnonin Shiyyar ke bayar wa abin farin ciki ne, inda ya ƙara da cewa hakan ya ƙara samar da zaman lafiya da kaunar juna ga mazauna yankin ba tare da duba da bambancin addini ba.
Musa ya ƙara da cewa Shugaban NAHCON, Zaikrullah Kunle Hassan na bada gagarumar gudummawa wajen zamanantar da jigilar aikin Hajji domin jim daɗin alhazan Nijeriya a ƙasa mai tsarki.
Ya ƙara da cewa hakan ya samu ne sabo da shi Zikrullah mai ruwa da tsaki ne a harkar aikin Hajji.
Ya kuma yi kira ga alhazan ƙasar nan da su ɗauki aikin Hajjin na bana a matsayin na daban, duba da cewa shekaru biyu anka kwashe ba a yi aikin Hajjin ba.
Musa ya ƙara da cewa NAHCON ba ta tsammanin samun nakasu wajen jigilar Alhazai a filin jirgin saman Fatakwal, inda ya ƙara da cewa hukumar ba ta taɓa samu matsala da ga ɓangaren nan ba.