Shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, a jiya Juma’a, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar jigilar alhazai da wasu kamfanonin jirage guda uku na ƙasa.
Kamfanonin jiragen su ne Max Air, Azman Air da FlyNas.
Biyun farko kamfanonin gida Najeriya ne yayin da FlyNas kuma kamfanin jirgin sama ne na Saudi Arabiya, inda ya ke aiki kan tsarin kason jiragen sama tsakanin Saudiya da kasashen da ke halartar aikin Hajji.
Shugaban Hukumar NAHCON ya sanar da cewa tawagar ma’aikatan hukumar za ta tashi zuwa kasar Saudiyya a ranar 6 ga watan Yuni yayin da jirgin alhazai na farko zai tashi a ranar 9 ga watan Yuni daga Maiduguri, jihar Borno.
Kamfanonin jiragen sama guda bakwai; Max Air, FlyNas, Azman Air, Med-View Airline, Skypower Express, Westlink Airlines da Arik Air, ne su ka nemi a sahale musu su yi jigilar alhazai.
Bayan an kammala tantance wa ne dai wadanda aka zaba suka sanya sunayensu guda uku da aka mika sunayensu ga fadar shugaban kasa domin amincewa da su kafin kulla yarjejeniyar kwangilar.
Jihohin da aka ware wa kamfanonin jiragen sama sun haɗa da: Max Air zai yi jigilar maniyyata daga jihohi 13 da suka hada da Adamawa, Bauchi, Benue, Borno, Gombe, Jigawa, Katsina, Kogi, Kwara, Nasarawa, Niger, Plateau da Taraba.
Kamfanin na Azman Air zai yi jigilar alhazai daga jihohi 16 da na rundunar soji. Jihohin sun hada da Kano, Abia, Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Cross River, Delta, Ebonyi, Ekiti, Enugu, Imo, Kaduna, Ogun, Ondo, Rivers, da Yobe.
A halin da ake ciki, FlyNas zai yi jigilar maniyyata daga Edo, FCT- Abuja, Legas, Osun, Oyo, Sokoto, Kebbi, da Zamfara- masu jihohi takwas.
A nasa jawabin, babban jami’in hukumar NAHCON ya taya kamfanonin jiragen sama da suka samu nasara, sannan ya umarce su da su yi wa dukkan maniyyata kulawar da ya dace da su.
Ya bayyana lokacin sanya hannu kan kwangilar a matsayin farkon ayyukan Hajji domin ba za a iya yin aikin Hajji ba tare da jigilar jiragen sama daga Najeriya ba.