Hajjin 2022: Mahukuntan Saudiyya sun fitar da sabbin dokoki ga kamfanonin jirage

0
266

Hukumar kula da harkokin sufurin jiragen sama ta ƙasar Saudi Arabiya, ta fitar da wasu sabbin dokoki ga kamfanonin jiragen da za su yi jigilar alhazai a Hajjin bana.

A cewar hukumar, dokokin sun shafi dukkan kamfanonin da za su yi aikin kai wa da kuma kwaso fasinjoji.

Haka kuma hukumar ta buƙaci kamfanonin da su tabbatar da cewa, maniyyatan da za su su kawo sun cika sharuɗan da aka basu dangane da lafiyar su.

Dokokin aka fitar ɗin sun haɗa da, tabbatar da cewa, maniyyatan na bana su kasance waɗanda ba su haura shekaru 65 da haihuwa ba, kana kuma sai sun kammala karɓar allurar rigakafin cutar korona.

Haka kuma dole maniyyatan su gabatar da shaidar gwajin da ke nuna cewa ba sa ɗauke da Corona, sananan a ji musu gwaji sa’o’i 72 kafin su tashi zuwa kasar ta Saudiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here