Hajjin 2022: Ƙungiyar Musulmai Mata ta kammala bitar alhazai mata a Katsina

0
398

Kungiyar Musulmai Mata (Association of Muslim women on Hajj oriatation and Islamic Da’awa 2022) a yau Talata ta kawo karshen bitar alhazai mata, inda ta koyar da miniyyata Aikin Hajiin bana a shiyyar Katsina.

Mallamai da sauran Shuwagabanni sun gabatar da jawabai masu mahimmanci a lokacin rufe bitar, kamar yadda sanarwa da ga kakakin Hukumar Alhazai ta Jihar Katsina, Badaru Bello Karofi ta rawaito.

Karofi ya ce uwar gidan gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Hadiza Aminu Bello Masari ta yaba da yadda ta ga Mlmaniyyatan cikin koshin lafiya, inda ta yi kira gare su da su yi amfani da abinda su ka koya, yanldda za su gudanar da aikin Hajjin cikin sauki.

Ta kuma yi kira ga maniyyatan da su yi wa mazajen su, ƴaƴan su da jihar su da kasarmu addu’a, tare da maida hankali wajen ibadar su domin samun Hajji karɓaɓɓiya.

A lokacin da ya ke gabatar da Jawabin sa a wajen taron, Babban Daraktan Hukumar Jin dadin Alhazai ta jihar Katsina, Alhaji Suleiman Nuhu kuki ya yaba wa ƙungiyar a kan yanda suke tallafa wa Hukumar Alhazai ta jihar katsina, musamman wajen gudanar da fadakar da maniyyata mata su fahinci abinda ya kamata su sani akan Aikin Hajj.

Ya kuma ci alwashin cigaba da tallafa wa kungiyar domin cigaba da gudanar da aikin su na fadakar da maniyyatan.

Alhaji Kuki ya ja kunnen maniyyatan jihar katsina a kan su yi amfani da abinda su ka koya cikin tsawon wata guda da suka yi subna koyon, yanda za su gudanar da aikin Hajjin su.

Haka Kuma ya yi kira ga maniyyatan da su zama jakadun jihar da kuma ƙasa baki ɗaya a lokacin da su ke a kasa mai tsarki.