Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta bayyana cewa kuɗin Hajji da Maniyyata su ka biya a bana ya ƙunshi dalar Amurka 800 na guziri, wato BTA.
A wata sanarwa da kakakin hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar, NAHCON ta ce kuɗin Hajjin bana na N2,496,815.29 ya ƙunshi dalar Amurka 800 a matsayin kuɗin guziri da a ka saba baiwa alhazai.