Hajjin 2022: Mun shirya tsaf domin fara jigilar alhazan Nijeriya gobe — Max Air

0
733

Kamfanin sufurin jiragen sama na Max Air ya ce ya shirya tsaf domin fara jigilar alhazai a Nijeriya domin aikin Hajjin bana da ga gobe Alhamis.

A tuna cewa Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON, ta sahale wa Max Air ya yi jigilar maniyyata dubu 16 na jihohi 13 na ƙasar nan zuwa aikin Hajjin na bana.

A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na kamfanin, Ibrahim Dahiru ya fitar, kamfanin ya lissafa jihohin da zai ɗebi alhazan su kamar haka : Adamawa, Bauchi, Gombe, Taraba, Kogi, Niger, Kwara, Jigawa. Katsina, Benue, Plateau, Borno da Nasarawa.

Ya ce Max Air zai yi amfani da jirage guda biyu ƙirar Boeing 747–400 domin jigilar alhazan.

Sanarwar ta ƙara da cewa an tanadi duk ma’aikatan kamfanin da na ɓangaren tashi da saukar jirgi domin fara jigilar.

“Kamfanin Max Air zai saka jiragen sa tun a farkon awannin ranar 9 ga watan Yuni a filin jirgin sama na Maiduguri , Jihar Borno domin fara tashin alhazai,” in ji sanarwar.