YANZU-YANZU [Hajj 2022]: Jirgin farko na alhazan Nijeriya ya tashi zuwa Saudiya

0
667

Jirgin farko na alhazan Nijeriya ya tashi zuwa Saudi Arebiya domin gudanar da aikin Hajjin 2022.

An yi bikin ƙaddamar da fara jigilar alhazan na Nijeriya a yau Alhamis a garin Maiduguri da ke jihar Borno.

Jirgin farko, na kamfanin Max Air, shine ya fara jigilar alhazan bana, inda ya kwashi sama da alhazai 500 zuwa ƙasa mai tsarki.

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Umara Zulum, shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON da sauran manyan baƙi ne su ka shaida tashin jirgin na farko a Hajjin bana.

Independent Hajj Reporters ta rawaito cewa jami’an Nijeriya na can Madina domin tarbar alhazan.