Rukunin farko na maniyyatan Abuja 347 sun tashi da ga filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe zuwa ƙasa mai tsarki domin aikin Hajjin bana.
Maniyyatan sun tashi ne a jirgin saman FLYNAS mai lamba XY5002.
Ƙididdigar da sashen bada umarni ma NAHCON ya bayar ya bayyana cewa a jirgin akwai maniyyata maza 171 da mata 176, tare da ma’aikata 23.
NAHCON ta bayyana cewa a halin yanzu an ɗebi maniyyata 1,354.