Jirgin ruwa maƙare da tumaki ya nitse a tekun Sudan kan hanyarsa ta zuwa Saudiya

0
574

Wani jirgin ruwa da ke ɗauke da dubban tumaki ya nitse a tekun Sudan a kan hanyar sa ya zuwa ƙasar Saudi Arebiya, inda dukkan dabbobin su ka hallaka, amma matuƙa jirgin sun tsira da rayukansu, kamar yadda hukumomi su ka bayyana.

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ya nitse ne a yankin Suakin ne tekun Sudan a kan hanyarsa ta zuwa Saudiya.

“Jirgin, mai suna Badr 1 ya nitse ne a awannin farko-farko na yau Lahadi,” in ji wani jami’in tashar kaya ta Ruwa na Sudan, wanda ya nemi a sakaye sunansa.

“Jirgin ya ɗauki awaki 15,800 sama da iya nauyin kaya da ya saba ɗauka,” in ji jami’in.

A ko wacce shekara na yo safarar tumaki da ga ƙasashen maƙwabta domin hadaya da mahajjata su ke yi a yayin aikin Hajji.

Jami’in ya yi gargaɗi cewa “da yi wuwar a samu cututtukan muhalli daina da yawan tunanin da su ka nitse a cikin ruwan,”