Hukumar alhazai ta Kaduna ta umarci maniyyatan Giwa, Soba, Lere da Kagarko domin tashi zuwa Saudiyya

0
651

Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna na sanar da maniyyatan Kananan Hukumomin Giwa, Soba, Lere, da Kagarko cewa su tuntubi Jami’an su na Kananan Hukumomi, wato Registration Officers, domin jin wadanda za su hallara a sansanin Alhazai dake Mando – Kaduna, da karfe 5.00 na yamman yau Laraba domin shirin kwashe su zuwa Ƙasa Mai Tsarki.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa daga Salisu Sani Anchau, Jami’in Hulda da Jama’a, a madadin Babban Sakatare na Hukumar Alhazai ta jihar Kaduna.

Sanarwar ta ce wajibi ne ga dukkan maniyyatan su sanya Uniform din su a lokacin da za su bar garuruwan su.

Zangon farko da Maniyyatan za su shiga idan sun isa Sansanin Alhazan shine dakin shan magani. Haka kuma Maniyyatan su zo da katin su na Asibiti da katin shaida, watau I.D. Card.

Hukumar Alhazan ta shawarci sauran maniyyatan Kananan Hukumomi na Jihar da su dinga sauraron gidajen rediyo domin jin lokacin fitowar su, inda ya ƙara da cewa “kada wani Maniyyaci ya je Sansanin Alhazai ba tare da ya ji lokacin fitowar sa ba.”