Hajjin bana: Alhazan Nijeriya 9,082 sun samu izinin shiga Rawdah

0
707

Dubban alhazan Nijeriya ne su ka samu shaidar izinin shiga kabarin Ma’aiki wato Raudah, da ke Masallacin Harami na Madina.

A wani takaitacciyar sanarwa da ga sashen yaɗa labarai na Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON, a ƙalla shaidar izinin shiga Rawdah 9,082 a ka baiwa alhazan Nijeriya.

Sanarwar ta ce dubban alhazan Nijeriya ne su ka samu nasarar shiga Raudah, a ƙarƙashin wani sabon tsari mai suna Tafweej da Saudi Arebiya ta ƙirƙiro da shi.

Sanarwar ta ce tsarin zai ci gaba da gudana a yayin da alhazan ƙasar ke ci gaba da sauka a birnin na Madina.