Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Katsina ta raba guzuri ga maniyyatan aikin Hajjin 2022 jirgi na farko da suka fito daga Ƙananan Hukumomin Kankia, Daura, Mani da kuma Kafur yayin da s ke shirin kwashe su zuwa ƙasa mai tsarki.
Babban Daraktan hukumar, Alhaji Suleiman Nuhu Kuki, kafin ƙaddamar da fara rabon guzurin ga maniyyatan, ya yi kira gare su da kada su yi wasa da guzurin su tare da zama masu ɗa’a a duk inda su ka tsinci kansu tun daga gida har zuwa kasa maitsarki.
Amirul Hajj na jihar a bana, Babban Jojin Jihar Katsina, Justice Musa Danladi Abubakar, tare da Kuki da sauran masu ruwa da tsaki a kan aikin Hajjin 2022 ne su ka zagaya domin tabbatar da komai na gudana kamar yadda ya kamata.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Badaru Bello Karofi, a wata sanarwa ya ce, Amirul Hajj ne ya kaddamar da fara bada guzurin ga maniyyatan, wanda sune jirgin farko da za su fara tashi daga jihar Katsina a bana.