Babban Ofishin Hukumar Tsaron Al’umma ta Saudi Arebiya ya tabbatar da hana shigowa da kuma amfani da kowane nau’i ko girma na iskar gas din dafa abinci a sansanonin mahajjata da kuma ofisoshin hukumomin gwamnati da ke cikin wurare masu tsarki.
Hukumar tsaron ta bayyana cewa haramcin zai fara aiki ne daga safiyar ranar daya ga watan Zul-Hijjah.
Matakin na hana shiga da kuma amfani da gas ɗin a wurare masu tsarki a lokacin aikin Hajji zai kasance tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro.
Hukumar ta yi gargadin cewa za a kwace duk wasu abubuwan da aka haramta, wadanda suka hada da murhu da tukunyar gas da za a iya amfani da su wajen dafa abinci, tare da jaddada cewa za a yi amfani da hanyoyin da doka ta tanada kan duk wanda aka samu ya saɓa dokokin nan.
Tawagar da ke sa ido kan kashe gobara ta hukumar za ta gudanar da rangadi na musamman a dukkan ofisoshin hukumomin gwamnati da cibiyoyin kasuwanci a wurare masu tsarki don tabbatar da cewa ba a yi amfani da gas a harabar su na Mina, Muzdalifah da Arafat a lokacin aikin Hajjidon tabbatar da lafiya, lafiya da amincin mahajjata.
Matakin hana amfani da gas ɗin dafa abinci daga wurare masu tsarki ya zo ne bisa tsarin kariya da hukumar ta sanya na rage afkuwar gobara a sansanonin mahajjata, da kuma lokacin zaman mahajjata a can.