Babban Lauyan kasar Saudiyya ya fitar da wani kakkausan gargaɗi game da raba kayan abinci da ake ganin yana da illa ga lafiya a tsakanin mahajjata.
An haramta sayar da ko rarraba kayan abinci gurɓatattu ga mahajjata, inda ofishin Babban Lauyan ƙasar ya ce duk wanda aka samu da aikata hakan za a hukunta shi.
Ana daukar keta dokokin kula da ingancin abinci a matsayin babban laifi kuma za a kama wanda ya aikata laifin, in ji ofishin.
Idan aka same su da laifi, wadanda suka karya dokokin kiyaye abinci za su fuskanci dauri har na tsawon shekaru 10 da kuma tara har zuwa Riyal miliyan 10 sannan za a soke lasisin masu aikata hakan kuma za a hana su yin duk wani aiki da ya shafi abinci.
Bugu da kari, wadanda kotu ta samu da laifi za a kunya ta su ta hanyar yaɗa sunayensu a kafafen yada labarai.
Ofishin ya lura da cewa, yana gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi na saɓawa ka’idojin kiyaye abinci, kamar yadda sashi na 36 na dokar abinci ya tanada.