Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna na sanar da maniyyatan Kananan Hukumomin Kaduna ta Arewa Watau Kaduna North, Kudan, Kaura, Zangon Kataf, Sanga, Kachia, da Chikun, cewa su tuntubi Jami’an su na Kananan Hukumomi, da aka fi sani ds Registration Officers, domin jin wadanda za su hallara a sansanin Alhazai dake Mando – Kaduna, da karfe 1.00 na ranar yau Asabar 25/6/2022 domin shirin kwashe su zuwa Kasa Mai Tsarki.
Wajibi ne ga dukkan maniyyatan su sanya Uniform din su a lokacin da za su bar garuruwan su, in ji wata sanarwa da Salisu Sani Anchau, Jami’in Hulda da Jama’a ya fitar
Zangon farko da maniyyatan za su shiga idan sun isa sansanin Alhazan shine dakin shan magani. Haka kuma Maniyyatan su zo da katin su na Asibiti da katin shaida, watau I.D. Card.
Hukumar Alhazan na shawartar sauran Maniyyatan Kananan Hukumomi na Jihar Kaduna da su dinga sauraron gidajen rediyo domin jin lokacin fitowar su. Kada wani Maniyyaci ya je Sansanin Alhazai ba tare da ya ji lokacin fitowar sa ba.