Hajjin bana: Matsalar biza ce ta kawo tsaiko a jigilar alhazan Bauchi — Hukumar Alhazai

  0
  331

  Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Bauchi ta danganta jinkirin da a ka samu a jigilar alhazan Jihar Bauchi da matsalar tsarin biza.

  Babban Sakataren hukumar, Imam Abdurrahman Ibrahim Idris ne ya bayyana haka a yau, inda ya ce matsalar ta shafi ɗaukacin jihohin Nijeriya.

  Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwar da Muhammad Sani Yunusa,
  Jami’in Yaɗa Labarai na hukumar ya fitar a yau Lahadi.

  A cewar sanarwar, Imam Idris ya yi kira ga maniyyatan da su ka rasa jirgin su na farko ko na biyu ko na uku da su zo hukumar domin tabbatar da sunayensu da aka liƙa, inda ya ƙaryata raɗe-raɗin da ake yi na cewa jerin sunayen da aka liƙa ne na karshe.

  Ya yi bayanin cewa jihar Bauchi ta samu biza na mahajjatan ta sama da 1400 sannan kuma ta yi nasarar jigilar maniyyata Bauchi kimanin 1310 zuwa ƙasa mai tsarki.

  Iman Idris ya jaddada cewa hukumar, ta hannun Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON tana tuntuɓar karamin ofishin jakadancin Saudiyya domin neman ƙarin biza domin ɗaukar dukkan sauran maniyyatan.

  Don haka ya bukaci maniyyatan na jirgin karshe da ba su ga sunayensu ba da su kara hakuri da jinkirin sama musu bizar, Inda ya Kara da cewar Hakuri ga Dan Adam za ta samar masa lada mai tsoka.

  Da yake bayyana aikin Hajji a matsayin amsa kiran Allah, Imam Abdurrahman ya yi amfani da wannan damar wajen kara yin kira ga jama’a da su himmatu wajen yin addu’a ga duk wata matsala da ka iya shafar aikin Hajjin bana.