Kimanin maniyyata 545 da ga jihar Katsina ne suka tashi daga filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua zuwa kasa maitsarki.
A wata sanarwa daga Jami’in Yaɗa Labarai na Hukumar Jin daɗin Alhazai ta Katsina, Badaru Bello Karofi da ya aikewa Hajj Reporters, maniyyatan su ne rukuni na biyu na jihar
Sanarwar ta ce jirgin, wanda ya tashi da misalin karfe 3.51am yanzun haka sun sauka filin sauka da tashi na King Abdulazeez International airport Jeddah lafiya kalau.
Amirul Hajj na jihar, justice Musa Danladi Abubakar tare da Babban Daraktan Hukumar Alhaji Suleiman Nuhu Kuki sun Yaba da kwazo ga jami,’an dake gudanar da tantance maniyyatan cikin lokacin batare da samun wata matsalaba, in ji sanarwar.
“Wannan shine karo na biyu da Ake samun Nasarar ta-da jirgin Alhazai cikin lokacin ba Kuma tare da samun wani tsaiki ba Wanda zaya Sanya jinkiri ga masu jiragen.
“Yanzun kimanin maniyyata 1,099 daga jihar katsina su ke a kasa maitsarki.
“A Wani labarin Kuma Alhazan jirgi na farko na Jihar katsina dake birnin Madina na cigaba da gudanar da ibadun su lami lafiya.
“Yanzun haka yawancin Alhazan guda 554 duk sun kammala ziyarar su kamar yanda Addinin musulunchi ya tanada.
“A Wani bangaren Kuma mallam da gwamnatin jihar katsina a karkashin Jagoranchin Rt.Hon Aminu Bello Masari ta dauki nauyin tura was Domin Alhazan jahar na cigaba da dada kar da maniyyatan yanda zasu guda nar da aikin Hajjin su Domin su Sami Hajj Mabrur,” in ji sanarwar.