Maniyyata daga Ƙananan Hukumomin Rano, Kura, Bunkure, Dawakin-Kudu da Ajingi da wasu daga cikin Jami’an Hukumar Jin daɗin Alhazai ta Jihar Kano
ne za su tashi zuwa ƙasa mai tsarki.
Hajj Reporters ta jiyo cewa a yanzu haka maniyyatan na Kananan Hukumomin da aka lissafa su na karɓar takardu na shedar izinin shiga kasar ta Saudiya, da sauran takardu na tafiyar cikin tsari da kwanciyar hankali.
A ɗaya bangaren Kuma maigirma Babban Sakataren Hukumar, Muhammad Abba Dambatta ya na ta kai kawo daga sansanin hukumar da filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano domin tabbatar da cewa maniyyatan sun tashi zuwa ƙasa mai tsarki cikin kwanciyar hankali.