Hajjin bana: Rukunin farko na alhazan Kano 339 sun sauka a Madina

0
243

Rukunin farko na alhazan Kano su 339 ya sauka a birnin Madina.

Maniyyatan sun tashi da ga filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da tsakar daren jiya a jirgin Azman Air mai lamba ZQ2360.

A na sa ran tuni ma maniyyatan samun sauka a Madina.

Hajj Reporters ta jiyo cewa wannan adadin na maniyyatan Kano ya sanya adadin alhazan Kano da a ka kai kasa mai tsarki ya zama 19,343.