Gwamnatin jihar Legas ta ce za ta mayar wa da maniyyata aikin Hajji kuɗaɗen su da suka biya amma basu samu kujera ba a Hajjin bana.
Kwamishinan harkokin cikin gida, Prince Anofiu Elegushi, ne ya bayyana hakan a jiya Talata yayin wani taron manema labarai a cibiyar ‘yan jarida ta Bagauda Kaltho da ke Alausa, Ikeja.
Elegushi ya ce za a mayar wa da waɗanda abin ya shafa kuɗaɗen su cikakku, inda ya ƙara da cewa za a yi biyan cikin tsari da kuma gaggawa.
Ya ce gwamnatin jihar Legas za ta buga sunayen maniyyatan da abin ya shafa a a jaridun ƙasa a matsayin rukunin farko na aikin Hajjin 2023.
A cewarsa, gwamnati za ta kuma dakatar da sayar da fom na aikin Hajjin 2023, har zuwa lokacin da za a tabbatar da ainihin adadin kujerun da za a bayar.
Kwamishinan ya tabbatar wa dukkan maniyyatan jihar goyon bayan gwamnatin jihar a kowane lokaci tare da addu’ar Allah ya dawo da alhazan da aka riga aka yi jigilarsu gida lafiya.