Maniyyata sun yi zanga-zanga a Kano bisa rashin samun kujerar zuwa aikin Hajji

0
316

Ɗaruruwan maniyyata ne su ka gudanar da zanga-zangar lumana a Kano kan rashin basu gurbin zuwa aikin hajji duk da cewa sun biya cikakken kuɗin aikin hajjin.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, masu zanga-zangar sun mamaye babban ofishin bankin Jaiz, kafin daga bisani su wuce zuwa ofishin hukumar alhazai ta jihar Kano.

Mutanen da abin ya shafa sun kai su 284, inda su ka ce sun yi matukar kaduwa da gano cewa bayan sun biya, babu wata kujera da aka tanadar musu, ganin cewa wasu daga cikinsu sun shiga shirin Adashin Gata na Hajji tun daga shekarar 2019.

Ɗaya daga cikin maniyyatan da abin ya shafa, Auwalu Jibrin ya ce, “Mu ne hukumar alhazai ta ƙasa ta bukaci mu buɗe asusu a bankin Jaiz, mu saka kuɗaɗen mu a can. Hukumar alhazai ta jiha ta karbi fasfo dinmu ta tantance mu, yanzu mun samu labarin cewa ba mu samu kujera ba.

“Yanzu an bar mu a maƙale ba tare da wani tabbaci ba. Bankin Jaiz ya shaida mana cewa tabbas akwai matsala kuma suna ƙoƙarin shawo kan matsalar.”

Majiyoyi da ke da masaniya kan lamarin sun shaida wa Daily Trust cewa an aika sunayen fusatattun maniyyatan zuwa hukumar alhazai ta jiha tare da rubuta bayanai amma ba a saka su a aikin hajjin bana ba saboda ragin kason da aka samu.

Shi ma a nasa bangaren, Babban Sakataren Hukumar Alhazai ta Kano, Abba Dambatta, ya shaida wa Daily Trust cewa hukumar na yin iya kokarinta don ganin an shawo kan matsalar, inda ya ce a bana, ba a sanya wadanda ke cikin tsarin Adashin Gata na Hajji, musamman ta bankin Jaiz a cikin waɗanda za a baiwa kujerar Hajji ba.

Sai dai ya ce zai je Abuja ne domin yin kokari wajen ganin an ware wa maniyyata 284.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa an kwashe rukunin farko na maniyyata 400 daga jihar Kano zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2022 a jiya Litinin.