Rukuni na 2 na maniyyatan Kano sun tashi zuwa Saudiyya

0
406

Rukuni na biyu na maniyyatan jihar Kano sun tashi daga filin jirgin saman Aminu Kano zuwa birnin Madina na kasar Saudi Arebiya.

Babban Sakataren hukumar, Alhaji Mohammad Abba Dambatta ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai a Kano.

Ya ce wadanda aka kwaso a zango na biyu sun hada da mahajjata daga karamar hukumar Fagge, ma’aikatan hukumar, malamai, da sauran jami’an hukumar.

Dambatta ya ce jirgin ya tashi ne da misalin karfe 8 na safiyar yau Alhamis.

Babban Sakataren ya umarce su da su kasance jakadu nagari tare da yi musu addu’ar samun zaman lafiya a jihar Kano da kasa baki daya.