Hukumar kula da Zirga-zirgar Jiragen sama ta Saudiya, GACA, ta amince da tsawaita wa’adin sauka a filayen jiragen ta ga masu jigilar alhazan Najeriya, a ƙarƙashin inuwar Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON.
A wata sanarwar da Jami’ar Hulɗa da Jama’a, Fatima Sanda Usara ta fitar a yau Litinin, an tsawaita wa’adin da ga yau 4 ga watan Yuli zuwa 6 ga wata ga ɗaya daga cikin kamfanonin jiragen saman, yayin da 4 da 5 ga wata aka amince da sauran.
Hukumar ta NAHCON ta buƙaci ƙarin wa’adin ne domin ta samu damar jigilar sauran alhazanta da su ka rage zuwa Saudiya domin aikin Hajjin 2022.
Sanarwar ta ce daga cikin maniyyata 43,008 da ake sa ran za su iso ƙasar Saudiyya daga Najeriya, 27,359, da suka haɗa da ma’aikata 527 da mambobin kwamitoci da shuwagabannin hukumar, tuni su na kasar Saudiyya a ƙarƙashin kason gwamnati.
Hakazalika, sama da 5,000 daga cikin maniyyata 8,097 ƙarƙashin kamfanunuwan sufurinmasu zaman kansu, kuma waɗanda suke da ingantacciyar biza an kwashe su zuwa ƙasa mai tsarki ta jiragen da aka tsara da sauran shirye-shirye.
An wajabta tsawaitawa ne sakamakon soke tashin jirgin sama da a ka yi da yawa a wannan karon, in ji sanarwar.