YANZU-YANZU: Za a fara kwaso alhazan Nijeriya zuwa gida a ranar Friday

0
531

A ranar Juma’a, 15 ga watan Yuli ne za a fara jigilar maniyyatan Nijeriya da ga ƙasar Saudiyya zuwa Nijeriya.

Shugaban Hukumar NAHCON, Barista Zikirullah Kunle Hassan ne ya bayyana hakan a yau Laraba, yayin taron bayan Arafat da ke gudana a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya.

“Da zarar GACA ta amince, jirgin za a fara jigilar alhazan zuwa gida Nijeriya daga ranar Juma’a 15 ga Yuli,” in ji Shugaban.