Hajjin bana: Buni ya raba wa alhazan Yobe Riyal ɗari uku-uku

0
347

Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni, ya bayar da gudummawar Riyal 300 na ƙasar Saudiyya ga kowane mahajjaci da mahajjaciyar jihar da su ke gudanar da aikin Hajjin 2022.

Shugaban Hukumar Alhazai ta jihar, Alhaji Bukar Kime ne ya baiyana hakan ga manema labarai a yau Juma’a a filin Arfa.

Ya ce an raba kyautar kuɗin ne domin rage wa alhazan jihar raɗaɗin tsadar rago domin yin hadaya, wato yanka dabba a yayin aikin Hajji.

Kime ya yi kira ga alhazan jihar da su maida hankali wajen gudanar da addu’o’i na musamman a wannan rana ta Arafat ga Jiha da ma kasa baki daya.

Ya kuma tuna cewa Gwamna Buni ya yi irin waɗannan hidimomin a aikin Hajjin da ya gabata an 2019.