Alhazan Jihar Katsina sun yaba da ingancin Abinci da Hukumar Alhazan jihar Katsina ke ba su a Makkah.
Wannan yabo ya zo ne sakamakon jin ra’ayoyin wasu daga cikin mahajjantan na jihar a birnin Makkah, bayan kammala aikin Hajji.
Wata mahajjaciya, Sa’adiyya Hamisu, ta ce tsabta da ɗanɗano, tare da tsarin girkin abincin, musamman na gargajiyar Hausa irin su tuwo da miya kala-kala ke sa tana ji kamar a gida take.
Ta ƙara da cewa tsarin ciyarwar na da matuƙar gamsarwa.
A nasu ra’ayin, Adamu Ibrahim da Abubakar Ashiru Ashura, sun ce yawa da ɗanɗano na ire-iren abincin da ake ba su abin yabo ne.
Sun godewa Gwamna Aminu Bello Masari kan karimcin da ake nuna masu.
Alhazan na bana, sun dukufa addu’ar neman zama lafiya da karuwar Arziki ga Nigeria, kafin komawarsu gida.