Daga Mustapha Adamu
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya raba wa alhazan jihar kuɗin kasar Saudiyya, Riyal Hamsin-Hamsin domin yin wasu bukatu kafin dawowar su gida Nijeriya.
Babban Sakataren Hukumar jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Muhammad Abba Dambatta ne ya sanar da hakan ga alhazan jihar yayin da ya kai musu ziyara a garin Makka.
Ya ce gwamnan ya bada wannan tagomashi ne domin alhazan su samu ma siyan katin waya da sauran buƙatu.
Dambatta ya kuma bayyana cewa zai umarci wakilan alhazan na shiyya-shiyya da su bi su gida-gida su raba musu kuɗin.
Ya kuma hori alhazan da su bi ƙa’idar sanya kaya da bai wuce nauyin kilo 32 ba, inda ya hotel su da su cika alkawuran su na yi wa ƙasa Nijeriya da jihar Kano addu’a.