Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Taraba ta sanar da ɓatan wata mahajjaciyar ta, Hajiya Hassana Abdullahi Bamusa a garin Makka.
A wata takaitacciyar sanarwa da Kakakin hukumar ya fitar a garin Makka a yau Talata, Hassana, ƴar Ƙaramar Hukumar Ibi, na ɗauke da fasfo mai lamba A-11801527.
A cewar sanarwar, Hassana na fama da matsalar makuwa.
Sanarwar ta ce duk wanda Allah Ya sa ya gan ta ko ji labarin inda ta ke, ya tuntuɓi kakakin hukumar a kan lambar waya 0595615192.