Hukumar Alhazan Sokoto ta umarci mahajjata da su duba sunayensu domin kwasosu zuwa Nijeriya

0
163

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Sokoto na kira ga mahajjatan jirgi na farko da suje su duba sunayensu a bakin masaukinsu.

Hukumar ta ce da zarar alhaji ya ga sunanshi ya tabbata gobe da yayi sallar Jumu’a ya yi dawafin bankwana kafin karfe ukku na rana.

A sanarwar da hukumar ta fitar ta bakin Yakubu Ayuba Gidan Igwai ta ce karfe uku na rana za su bar masauki zuwa jidda domin komawa gida Najeriya.