Sama da alhazai 170,000 ne suka ziyarci Madina bayan kammala aikin Hajji a Makka

0
284

Kimanin alhazai dubu 171 ne suka isa birnin Madina bayan kammala aikin hajji a birnin Makkah, in ji Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiya a jiya Asabar.

Kididdiga daga ma’aikatar Hajji da Umrah ta nuna cewa cibiyar kula da shige da fice ta Madina ta karbi baƙi sama da 160,000 da suka isa ta mota.

Haka-zalika kusan 8,000 daga cikin su ne cibiyar karbar alhazai ta kasa ta tarba, inda sama da 3,000 sun yi tafiya a kan babban titin jirgin kasa na Haramain.

Alkaluman ma’aikatar sun kuma bayyana cewa, dubban maniyyata ne suka bar Madina zuwa kasashensu, yayin da kusan 74,000 suka rage a birnin.