Zuwa yanzu dai alhazan jihar sun cika da murna yayin da Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta jihar Kano ta bayyana gobe Alhamis a matsayin ranar da za’a fara aikin jgilar dawo da alhazan gida Najeriya.
Haka kuma a ranar 31 ga wata za’a akai alhazan jirgin karshe zuwa birnin Madina.
Babban Sakataren Hukumar Ambasada Muhammad Abba Danbatta ne ya bayar da tabbacin haka a garin Makkah a yau Laraba.
Ya ce dukkanin shirye-shirye sun kammala domin fara kwasar alhazan zuwa gida Nijeriya.