Rukunin farko na Alhazan Kano 260 sun dawo gida Nijeriya

0
314

Rukunin farko na Alhazan jihar Kano 260 da su ka yi aikin Hajjin bana sun dawo gida Nijeriya a jiya Juma’a da rana.

Alhazan, waɗanda su ka dawo a jirgin Azman ZQ2349, sun sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke jihar Kano da misalin ƙarfe 2:41 na rana.

Babban Sakataren Hukumar, Muhammad Abba Dambatta ne ya shida hakan ga manema labarai a jiya Juma’a a Makka.

Dambatta ya tabbatar da cewa alhazan masu da’a da biyayya ne a lokacin zaman su a ƙasa mai tsarki.

Ya kuma godewa gwamnatin jihar Kano bisa goyon bayan ta a lokacin aikin Hajjin da bayan sa.

Hakazalika, a safiyar yau Asabar, Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta bada sanarwar cewa tuni wani jirgin na Azman, mai lamba ZQ2351 ya kwaso rukuni na biyu, ɗauke da alhazai 390 zuwa jihar Kano da ga filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa ma King Abdulaziz, Jeddah, zuwa Kano.