Hukumomin Saudiyya sun cire shingen da suka sanya don hana alhazai tabawa da kuma sumbatar Al-Hajar Al-Aswad da kuma Kaʿabah.
An cire kariyar ne wadda ta kewaye Ka’abah wadda aka sa a lokacin annobar korona domin hana mutane, yayin da aka fara aikin Umrah.
Ana ta yada hotunan masu ibadah da suke ta kokarin taba Al-Hajar Al-Aswad din.
A farkon shekarar nan hukumomin kasar ta Saudi Arabia suka janye yawancin matakan kariyar da suka sanya na kokarin dakile annobar korona.
Aikin Hajjin da aka kammala a watan da ya gabata ya kasance kusan yadda ake yi a shekarun baya kafin daukar matakan kariya na korona, bayan shekara biyu da ta tsauraran matakai da aka dauka na rage yawan mahajjata.