Hajjin 2022: Mun kammala dawo da alhazan Nijeriya gida — NAHCON

0
310

Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta ce ta kammala jigilar dawo da alhazan Nijeriya gida bayan kammala Ibadar aikin Hajjin bana.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’ar yaɗa labarai ta hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar a yau lahadi.

A cewar Usara, jirgin Azman ne ya kwaso rukuni na ƙarshe na alhazan su 319, wadanda suka hadar da Alhazan jihar Kano dana Kaduna da kuma jami’an na NAHCON, inda ya ɗauko su daga filin Jirgin Sama na Sarki Abdul’aziz dake Jidda da misalin karfe 12 na ranar yau Lahadi.

Sanarwar tace Shugaban Hukumar ta NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya danganta nasarar da suka samu ga Allah da kuma ƙoƙarin gwamnatin Shugaban Ƙasa, Muhammad Buhari saboda irin goyon baya da haɗin kan da yake baiwa hukumar.

Ya kuma danganta matsalolin da suka samu yayin jigilar kai alhazan kasa mai tsarki daga nan Nijeria da cewa rashin wadataccen lokaci, da wasu matsaloli da suka dha kan al’ummar.

Zikrullah kulle Hassan ya kuma bada tabbacin zasu fara shirye-shiryen aikin Hajjin baɗi a da wuri don magance matsalolin da aka fuskanta a bana.