Hajjin 2022: Wani Alhaji daga cikin alhazan Kano ya rasu a Makkah

0
211

Hukumar Kula da Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rasuwar ɗaya daga cikin alhazanta na Hajjin bana, Sani Idris Mohammed a garin Makkah.

A wani sako da Babban Sakataren hukumar, Abba Muhammad Dambatta ya aike wa Hajj Reporters, ya ce marigayin ya fito ne da ga Ƙaramar Hukumar Madobi.

A cewar Dambatta, marigayin ya rasu a ranar Juma’a, sai dai kuma bai faɗi dalilin rasuwar ta sa ba.

Babban Sakataren ya ƙara da cewa tuni a ka yi jana’izar mamacin a Masallacin Harami na Makkah, sannan a ka binne shi a makabartar Shira.