Saudi Arebiya ta ce kawo yanzu, ta bayar da biza 85,000 domin gudanar da ummarar bana.
Mataimakin Ministan Hajji da Ummara, Abdulfattah Mashat, shi ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai.
Mashat ya ce kawo yanzu, sama da mutum 25,000 da aka amince da bizarsu sun ziyarci Saudiyya don gudanar da Ummara.
Sannan adadin izini (permit) da aka bayar ta manhajar ‘Eatmarna’ daga farkon lokacin da a ka buɗe kakar Ummara ta bana zuwa yau, ya kai 842,045.
Bayanan Mashat sun yi daidai da burin da Saudiyya ke da shi na ƙara bunƙasa ƙasar da ma sha’anin Hajji da Umurah ya zuwa 2030.
Burin ‘Vision 2030’ da Saudiyya ke da shi, shi ne kasar ta ga ta iya karɓar baƙuncin maniyyatan da ya wansu ya kai miliyan 30 tare da faɗaɗa hidimar da ta saba yi musu duk shekara
Ya kuma kara da cewa ba a ƙayyade adadin baƙin da za su shiga ƙasar don hajjin Umurah ba. Sai dai kuma akwai buƙatar maniyyata su bibiyi manhajar nan ta Eatmarna domin sanin lokuta da kuma yawan mutanen da Masallacin Harami zai ɗauka.
Ya na mai cewa maniyyaci na da damar yin Umurah fiye da ɗaya ba tare da fuskantar wasu sharuɗɗan hani ba ta hanyar amfani da manhajar Eatmarna.
Haka nan, da yake yi wa Asharq Al-Awsat jawabi, Mashat ya bayyana cewa Ma’aikatar Hajji da Umurah ta sauƙaƙe hanyar samun biza ga maniyyatan ƙetare don hajjin Umurah na bana wanda ya soma aiki daga ran 1 ga Muharram, 1444 wanda ya yi daidai da 30, Yuli, 2022.
Ya ƙara da cewa, abu biyu kawai ake buƙatar maniyyata su yi, wato miƙa buƙatarsu ta Umurah ta “Maqam,” kafin su zaɓi duka tanade-tanade da kuma tsare-tsaren da suke buƙata.
Ya ce maniyyata na da damar tsara yadda aikin Umurarsu zai kasance ta hanyar amfani da ɗaya daga cikin hanyoyin intanet da aka samar.
Bugu da ƙari, ya ce shirin ba da bizar Umurah ta manhajar Eatmarna, hakan zai kasance ne daidai da tanadin shirin kula da lafiya wanda hukumomin da lamarin ya shafa suka amince da shi don kula da lafiyar mahajjata da sauran baƙi don ba su damar aiwatar da Umurah cikin kwanciyar hankali da lumana.