Alhazan Katsina sun bayyana gamsuwarsu dangane da Hajjin 2022

0
228

Wasu daga cikin alhazan jihar Katsina suka bayyana farin cikinsu da kuma gamsuwa dangane da yadda Hajjin na bana ya kasance.

Alhazan sun baiyana cewa kaf Nijeriya babu wadanda jihar su ta yi musu hidima ingantacciya irin alhazan Katsina.

Alhaji Usman Sulaiman na daga cikin alhazan ƙarshen da suka dawo gida Katsina, kuma ya bayyana gamsuwarsa game aikin Hajjin inda ya ce, “Mun yi Hajji cikin kwanciyar hankali, kuma duk abin da muke buƙata Gamnatin Katsina ta samar mana da shi. Mun samu fifiko fiye da kowace jiha, mun ji daɗi ɗari bisa ɗari.”

Haka shi ma Alhaji Mu’azu Adamu ya ce, “Kaf Nijeriya babu alhazan da suka samu gata irin alhazan Jihar Katsina a Hajjin bana. An ba mu masauki kusa da Harami ta yadda ba mu wahala wajen samun sallah.”

Shi kuwa Alhaji Sulaiman Ahmad Kandarawa cewa ya yi, “Aikin Hajji ya kammala lafiya, gwamnati ta yi mana adalci. Kuma mun yi wa Nijeriya addu’ar samun shugabanni nagari.”

A nata ɓangaren, Hajiya Lariya Shuaibu ta ce “Abubu da dama sun burge ni dangane da Hajjin bana. Mun rungumi Ka’abah, lokacin da muka zo gab da an bude ta abin ya faranta mana rai sosai.”

“Alhamdu lillah, babu abin da ya fi burge ni kamar cire shingen ka’aba da aka yi. An samu shiga wurin a yi nafila raka’a biyu, sannan ka taɓa Ka’abah. An ba mu abinci, sannan Gwamnatin Katsina ta tallafa mana da Riyal ɗari uku-uku, mun gode,” inji Hajiya Aisha Umar.

Da alama dai alhazan Jihar Katsina sun samu kyakkyawar kulawa daga gwamnatin jihar duba da yadda alhazan suka bayyana gamsuwarsu game da Hajjin 2022 da suka samu zuwa.

Lamarin da ya sa suka yi wa Gwamnatin Katsina fatan alheri da kuma ci gaba da bai wa alhazan jihar irin wannan kula a ayyukan Hajji masu zuwa.

Idan dai ba a manta ba, kujerun Hajji 2,146 aka bai wa Jihar Katsina don Hajjin 2022 kamar yadda Gwamnan jihar, Aminu Bello Masari ya bayyana a farkon shirye-shiryen hajjin bana a Mayun da ya gabata.