Ƙungiya mai Zaman Kanta da ke sanya idanu da kawo rahotanni kan Hajji da Ummara, Independent Hajj Reporters (IHR) ta ce ta karɓi kashin farko na rahoton yadda a ka gudanar da aikin Hajjin bana da a ka kammala kwanan nan domin fara shirye-shiryen bikin bada kyaututtuka.
IHR ta ce ta ɗauki wasu ƙwararrun masu ruwa da tsaki a kan harkokin Hajji da kuma ƙwararru daga sassa daban-daban don taimakawa wajen tattara bayanai da ƙididdiga kan ƙwazon hukumomin alhazai na jihohi, kamfanonin jigilar Hajji da Ummara masu zaman kansu da kuma sauran masu ruwa da tsaki a Hajjin da a ka kammala.
Cikin sanarwar da shugaban ƙungiyar na kasa, Malam Ibrahim Muhammed ya fitar ranar Litinin ya ce, cibiyar na matuƙar godiya ga ƙoƙarin da tawagar ta yi wajen sauke nauyin da aka ɗora mata.
Haka nan, Muhammed ya yaba wa ƴan tawagar bisa jajircewar da suka nuna wajen tattara bayanai duk da an sanar da su a ƙurarren lokaci.
IHR ta ce za ta haɗa kai da sashen sanya ido da tabbatar da bin doka na Hukumar Hajji ta Nijeriya (NAHCON) wajen nazarin haɗin kan da aka samu kafin Hajji, haɗi da rahoton da ta karɓa kafin daga bisani ta fitar da waɗanda za a karrama da lambobin yabo.
Sanarwar ta ce tun bayan da aka assasa kafar a 2003, IHR kan yi nazarin ayyukan bayan kammala Hajji duk shekara domin yabawa gami da saka ƙaimi ga waɗanda suka yi aiki tuƙuru wajen yi wa alhazan Nijeriya hidima a lokacin Hajji a Saudiyya, daga farawa zuwa kammalawa.
Kazalika, IHR ta ce duk da ƙalubalen da ke tattare da Hajjin na 2022, wasu kwamitocin da NAHCON ta kafa da hukumomin alhazai na jihohi haɗa da kamfanonin sufuri da sauransu, sun yi iya ƙoƙarinsu wajen tabbatar da komai ya tafi daidai kamar yadda aka tsara wajen yi wa maniyyata hidima.
Za a iya tuna cewa bayan Hajjin 2019, IHR ta shirya taron Miƙa Lambar Yabo ga waɗanda suka yi zarra
wajen ayyukan Hajji, taron da ya samu mahalarta daga ciki da wajen Nijeriya.
Manyan baƙin da suka halarci taron a wancan lokaci da ya gudana a Abuja ciki har da; tsohon jakadan Saudiyya a Nijeriya, Marigayi Adnan Bostaji, wakilin gwamnan Yobe, Sanata Ahmad Baba Kaita, tsohon Shugaban NAHCON, Barista Abdullahi Mukhtar Muhammed, Shugaban Babban Taron Hajji da Ummarah na Duniya, Muhsin Tutla da sauransu masu yawan gaske.