Ma’aikatar Hajji da Ummara ta Saudi Arebiya ta ce, a cikin adadin mutanen da za su yi aikin Hajjin baɗi (2023), za ta bada kaso 26 cikin 100 ga tsofaffi da su ka haura shekaru 65 na haihuwa.
Shafin Haramain ya rawaito cewa ƙasar ta kuma ce za ta ɓullo da shirin biyan kuɗin yin aikin Hajji ta tsarin biya biyu.
Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa za ta soke tsarin zuwa hajji na mai-rabo-ka-ɗauka, inda za ta ƙyale ko wanne maniyyaci ya yi rijista kai tsaye.