Saudiyya za ta buɗe rajistar maniyyata aikin hajjin 2023 na cikin gida a watan Satumba

0
558

Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudi Arebiya ta ce a ranar 1 ga watan Satumba za ta buɗe fara rajistar maniyyata mazauna ƙasar don gudanar da aikin hajjin 2023.

Wannan dai shi ne karon farko da ma’aikatar za ta fara rajistar aikin Hajji da wuri.

Ma’aikatar ta gudanar da wani taro da hukumar kula da mahajjata na cikin gida, da wakilan dandalin tattaunawa kan harkokin kasuwanci a ranar Alhamis.

A taron, an tattauna hanyoyin yin rajistar mahajjatan cikin gida a wani ɓangare na fara shirye-shiryen farkon lokacin aikin Hajji, kamar yadda jaridar Okaz/Saudi Gazette ta bayyana.

Ma’aikatar na shirin gabatar da wani sabon ɓangare na huɗu a karkashin sunan “Economic 2”, wanda ya haɗa da gidaje a gine-gine a wajen Mina da kuma soke tsarin yin ƴar-tinƙe wajen zaɓar mahajjata.

Mahajjaci zai iya yin rajista a wurin kai tsaye, tare da kashi 25% na kujerun da aka keɓe don mahajjata da suka haura shekaru 65.

Sabon tsarin zai buƙaci biyan kudaden da aka kayyade kafin ranar 30 ga Jumada Al-Awwal 1444 (December 24, 2022) na biya-biyu.

Dole ne a biya kashi 72 cikin sa’o’i 72 na rajista, kuma za a iya biya cikon kashi na biyu har zuwa 30 ga Jumada Al-Awwal 1444.

Mahajjata masu zuwa bayan wannan rana za su biya gaba ɗaya cikin sa’o’i 72 na rajista.