Shugaban ƙungiyar Musulmi ƴan kasuwa (The Companion) na ƙasa, Injiniya Kamil Olalekan, ya yaba, tare da taya Shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Alhaji Zikrullah Kunle Hassan da tawagarsa murnar kammala aikin Hajji na 2022 cikin nasara.
Saƙon taya murnar na ƙunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da ƙungiyar ta fitar a Legas, mai ɗauke da sa hannun shugabanta.
Olalekan ya tuna yadda Hajjin bana ya kasance mai tattare da ƙalubalai, duba da yadda yanayin da NACHON da masu ruwa da tsaki a harkokin Hajji suka gudanar da ibadar ta bana.
Ya ce, “Da farko, Hajji ne da aka gudanar bisa taƙaitacciyar sanarwa da kuma gudanarwa haɗi da wasu sabbin tsare-tsare da dokokin da hukumomin Saudiyya suka ƙirƙiro.
“Haka nan, abin a yaba ne ganin yadda NAHCON ta kammala ayyukan Hajji ciki har da jigilar alhazai zuwa gida sati ɗaya kafin cikar wa’adin da Saudiyya ta gindaya,” inji Injiniya Olalekan.
Bugu da ƙari, ƙungiyar ta yaba da yadda Shugaban NAHCON ɗin ya yarda cewa lallai an samu ‘yan matsalolin da ba a rasa ba yayin jigilar maniyyatan Nijeriya zuwa ƙasa mai tsarki wanda hakan ya yi sanadiyar da damansu ba su samu yin Hajjin ba.
Wanda tuni hukumar ta ba da haƙuri kan haka tare da ba da tabbacin za a maida wa maniyyatan kuɗaɗensu da kuma ɗaukar matakan inganta ayyukan Hajji a gaba.
Olalekan ya ƙara da cewa, Alhaji Hassan mutum ne masanin makamar aiki wanda babu kokwanto dangane da irin nasarorin da yakan samar a duk inda ya tsinci kansa da aiki.
Ya ce Hassan tsayayye ne kuma jajirtaccen Musulmi wanda ke da ƙwarewa kan ayyukan Hajji gami da ilimin Ƙur’ani Mai Girma da Saunnar Annabi (SAW), masanin harshen Larabci da sauransu wanda hakan ya tabbatar da cancantarsa kan aikin da aka ɗora shi a kai.
Daga nan, ya ba da tabbacin ƙungiyarsu ta ‘The Companion’ na alfahari da shi da kuma nasarorin da ya samu kawo yanzu, tare da nuna ƙwarin gwiwar ƙwarewarsa za ta amfani ayyukan Hajji masu zuwa.
Kazalika, ya yi addu’a kan Allah Ya ci ga da lulluɓe shi fa rahmarSa shi da tawagarsa Ya kuma taimaka wa NACHON wajen sauke nauyin da ya rataya a kanta cikin nasara.
Idan dai za a iya tunawa, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa Alhaji Hassan a matsayin Shugaban NAHCON ne a Disamban 2019, inda aka rantsar da shi a Fabrairun 2020.